ABNA24 : Firai ministan rikon ya kuma kara da cewa zai kafa kwamiti wanda zai gudanar da bincike sosai a cikin abubuwan da suke faruwa a birnin Tripoli don hukunta wadanda suke da hannu cikin tashe tashen hankula wadanda suka yi sanadiyar raunata mutane akalla 100, daga ciki har da jami’an tsaron kasar, da kuma mutuwar mutum guda.
Wasu masana suna ganin tabarbarewar tattalin arzikin kasar da kuma dokar hana fita wacce gwamnatin kasar ta kafa don hana yaduawar cutar korona a kasar na daga cikin dalilan da suka jawo tashe-tashen hankula, a yayinda wasu kuma suna ganin, wasu dalilai sun tabbatar da cewa akwai hannun wasu ‘yan siyasa a cikin tada rikicin.
342/